Wednesday, 16 January 2019

Messi Ya Kafa Tarihin Da Babu Kamarsa A Laliga

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi, yakafa tarihin da babu wani dan wasa daya taba kafawa a gasar laliga tunb daga lokacin da aka fara buga gasar kusan shekaru sama da dari kenan.

Lionel Messi ya ci kwallaye 400 a gasar La Liga, bayan da Barcelona ta doke kungiyar kwallon kafa ta Eibar da ci 3-0 a wasan mako na 19 na gasar laliga da suka kara a ranar Lahadin da suka gabata.

Luis Suarez ne ya ci sauran kwallaye biyun daya bai wa kungiyar Barcelona damar samun maki biyar tsakaninta da wadda take mataki na biyu a teburin La Ligar bana wato kungiyar Atletico Madrid.

Da wannan kwallon da Messi ya ci ya tsawaita tarihin cin kwallaye a gasar ta La Liga bayan da dan wasa Cristiano Ronaldo ne keda kwallaye fiye da 300 a wasanni 435 da ya yi wa Real Madrid.

Messi wanda ya buga wa Barcelona wasa 22 a wannan kakar ta 2018 zuwa 2019 ya ci kwallaye 23, ciki har da kwallaye 17 da ya zura a raga a gasar La Liga, kuma shi ne kan gaba a ‘yan wasan da sukafi zuwa kwallo a kakar ta laligar Spaniya.

Barcelona za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Lebante a wasa na biyu na gasar cin kofin Copa del Rey a ranar 17 ga watan Janairu, a wasan farko dai Levante ce ta yi nasara da ci 2-1.

Duk Duniya Babu Kamar De Gea - Solskjaer

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer, ya jinjina wa mai tsaren ragarsu, Dabid De Gea bisa gagarumar rawar da ya taka a nasarar da suka samu kan Tottenham a gasar firmiyar Ingila, in da suka tashi 1-0.

Solskjaer da ke zama kociyan rikon kwarya a kungiyar ya bayyana, De Gea a matsayin gola mafi kwarewa a duk fadin duniya, yayin da ya ce, mai tsaron ragar na kokarin kafa tarihin da za a ci gaba da tunawa da shi a Manchester United.

Mai tsaren ragar ya kawar da kwallayen da dama da Tottenham ta kai hare-harensu musamman bayan dawowa daga hutun rabin lokaci inda ya hana kwallaye 11 shifa ragar United din kokarin da shima kociyan Tottenham yace yakamata a jinjinawa mai tsaron ragar.

“Tabbas dole jinjinawa De Gea saboda abinda yayi a kungiyar ya nunawa duniya cewa kawo yanzu babu mai tsaron ragar daya kaishi iya tsare raga kuma ya cancanta daya lashe kyautar gwarzon mai tsaron raga na duniya” in ji Solkjaer.

Dan wasa Marcus Rashford ne ya jefa kwallo daya tilo a fafatawar ta ranar Lahadi kuma shima ya kafa tarihin zura kwallaye a raga a wasanni uku a jere yayinda kawo yanzu ya zura kwallaye hudu sannan ya taimaka an zura uku a lokacin Solkjaer.

Gabanin Solskjaer ya karbi aikin horar da Manchester Unted, akwai tazarar maki 8 tsakaninta da Arsenal, amma a yanzu kungiyar ta kulle wannan tazarar, in da kowacce daga cikinsu ke da maki 41.

Kocin ya samu nasara a dukkanin wasanni shida da ya jagoranci kungiyar tun bayan maye gurbin Jose Mourinho a cikin watan Disamba wanda kungiyar ta kora sakamakon rashin kokari yadda yakamata.

Ba Za Mu Lamunci Sayen Kuri’a Ba –EFCC

Hukumar Yaki da Rashawa EFCC ta bayyana cewa, ba za ta amince da saye da sayar da kuri’a da wasu ‘yan siyasa su kan yi ba a yayin da ake gudanar da zabe ba, musamman a zaben dake tafe na 2019.

Mukadadashin shugaban sashin watsa labarai na hukumar, Mista Tony Orilade, ya bayyana haka a wani taro da aka yi wa lakabi da “Say No To Bote Buying” wanda aka gudanar a Abuja jiya Litinin.

Orilade ya ce, lamarin sayen kuri’a ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasa na sayan kuri’u daga jama’a masu jefa kuri’a maimakon su je su nemi shawo kan ra’ayin su ta hanyar gabatar musu da bayanan akida da ayuyukan da za su gudanar gare su.

“Lallai wannan babban laifi ne kuma ba za mu amince da shi ba saboda a kwai babbar matsala tattare da sayen kuri’a daga hannun jama’a.

“I dan ka sayar da kuri’arka kamar ka sayar da rayuwar ka ne gaba daya har na tsawon shekara hudu kuma ba zaka iya yin korafi a kan yadda ake gudanar da mulki ba don ka riga ka sayar da ‘yancinka.

“Ku zabi mutanen da kuke da imani da abin da zai yi muku, ku zabi mutumin da kuke gani zai kare mutuncinku kuma zai kare dukkan abin da ya shafe ku da sauran ‘yan kasa,” inji shi.

Mista Usen Asanga, babban jami’i a kungiyar ‘Youth Alibe Foundation’, ya ce yaki da dukkan wani nau’in laifi aiki ne na kowa da kowa.

Asanga ya kuma kara da cewa, yadda ake ci gaba da sayen kuri’u a tsakanin jama’a, abin nau’in barazana ne ga tsarin dimokradiyya a Nijeriya.

“Idan muka sayar da kuri’armu to bamu da wani karfin gwiwar da zamu iya tambayar shugabanin a kan yadda suka gabatar da mulkinsu.

“Yana matukar mahimmanci mu zabi mutane da muke da yakinin za su kare mana ra’ayinmu ta haka kuma za mu iya tunkarar su akan yadda suke gabatar da ayuyukansu musamamman in sun kauce hanya,” inni shi.

Ya kuma bukaci hukumar zabe INEC ta tabbatar da ta gudanar da sahihin zabe wanda zai samu karbuwa ga dukkan ‘yan Nijeriya.

Tun da farko, shugaban shirya taron, Olanrewaju Toriseju, wanda aka fi sani da “Ambassador Wahala”, ya bukaci matasa su guji bangar siyasa a lokacin yakin neman zabe da lokacin gudanar da zabe da kuma bayan an kammala zaben gaba daya.

“Mun zo don tunatar da jama’a ne a kan illolin saye da sayar kuri’a ta hanyar kade kadekadenmu da kuma wasan kwaikwayo,” inji shi.

Toriseju, dan danwasan barkwanci ne kuma dan rajin kare hakkin bil’adama ne ya kuma ce an samu tallafin hukumar EFCC wajen gudannar da taron gangamin.

Source: hausa.leadership.ng

Adamu Mohammed Ne Sabon Sufeton ‘Yan Sanda

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Mohammed Adamu matsayin sabon Sufeton ‘Yan Sanda na kasa.

Bayani na nuna cewa, in har ba a samu wani canji na gaggauwa ba fadar shugaban kasar za ta bayar da cikkaken sanarwa nadin yau Talata, wanda shi ne zai maye gurbin Ibrahim Idris wanda yake kammala aikinsa jiya Litinin.

Bayani ya nuna cewa, Shugaba Buhari ya yanke shawarar nada sabon sufeton ne bayan da aka ci gaba da samun matsin lamba daga jam’iyyun adawa in da suke korafin cewa, na neman a tsawaita aikin shugaban ‘yan sanda ne saboda a samu daman murde harkar zaben da za gudanar a cikin wannna shekarar.

Bayanin ya kuma ci gaba cewa, tuni shugaban kasar ya yanke shawarar wanda za nada a matsayin sufeto janar na ‘yan sandan ya kuma yanke shawarar rashin tsawaita zamanin aikin Idri Ibrahim da aikin nasa ke karewa.

Mista Mohammed, da aka fi sani da Mohammed Lafia, kafin wannan nadin shi ne mataimakin sufeto janar mai kula da yankin na 5 na rundunar ‘yan sanda na kasa.

Mista Mohammed, dan asalin garin Lafia, ya jijhar Nasarawa, an kuma haife shi ne a ranar 9 ga watan Nobamba 1961.

Ya shiga aikin dan sana ne a shekakar 1986. Ya kuma yi aikid a rundunar samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, ya kuma rike mukanin Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Inugu.
Source: hausa.leadership.ng

Monday, 14 January 2019

Labarin Yanda Wata Baiwar Allah Ta Samu Tsaida Da Sallah

Wata baiwar Allah ta bayar da labarin yanda ta yi fama da kokarin tsayar da Sallah shekaru 4 da suka gabata, tace ta fara da yin sallah daya a rana, watau Sallar Subahi.

Ta kara da cewa a haka a haka, wani lokacin ta yi akan lokaci wani lokacin kuma tayi bayan lokaci har ta samu yanzu tana tsayar da salloli 5 a rana.

Ta kara da cewa tana baiwa wanda ke fama da tsayar da sallah shawara da ya fara da kadan-kadan wataran zai samu tsayar da sallah biyar.

Ta karkare da cewa Allah ya sauwaka mana damar tsayar da salloli 5 a rana.

Kalli Wadda Ta Kirkiro Inkiyar Hannu Ta 4+4 Da Buhari Yayi

Inkiyar shugaban kasa, Muhammadu Buhari a neman sake zabenshi a zabe me zuwa itace 4+4 wadda masoyanshi ke daga hannaye sama da nuna yatsu hudu, da dama an amince cewa daga birnin Kano ne wannan inkiya ta samo asali, saidai ko wanene ya kirkirota? Me baiwa gwamnan Kano shawara ta fannin kafafen watsa labarai na zamani, Salihu Tanko Yakasai yace wannan matarce.

Salihu ya rubuta cewa, kasancewar inkiyar 4+4 ta zagaye Duniya, bari in gabatar muku da matar da ta kitkiri wannan inkiya a Kano a matsayin inkiyar gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Itace Hajiya Sa'adatu Babaji, tsohuwar shugabar gidan rediyon Kano wadda kuma a yanzu itace me baiwa gwamnan Kanon shawara ta musamman akan harkokin mata.

Dino Melaye Ya Na Kwance A Asibitinmu, In Ji Kakakin DSS

Jami’an tsaro na farin kaya ta (DSS) ta bayyana cewar ta kwantar da Sanata Dino Melaye a cikin asibitinta da ke Abuja domin ci gaba da samar masa da lafiya da kuma taimaka wa ‘yan sanda kan yanayin nasa.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Kakakin DSS, Peter Afunnaya ya fitar, yana mai bayyana cewar ‘yan sandan sun kawo Dino Melaye cikin asibitin DSS ne biyo bayan samun izinin tsareshi na kwanaki 14 wanda ya fara aiki tun daga ranar 9 ga watan Janairun 2019.

A cewar shi, “Abun da ya sanya aka kawo shi asibitinmu, shine domin taimaka wa ‘yan sanda wajen baiwa shi Sanata Dino kulawar jinya da yake bukata,” Inji Sanarwar Ya kuma kara da cewa, “Sanatan yana samun kyakkyawar kulawa ta kwararrun likitoci a sakamakon hadin kai da ake samu daga gareshi,” Inji DSS Peter Afunnaya ya ce, sun fitar da wannan sanarwar ne a bisa dole, domin warware shubuhar wasu bayanai na karya da suka basu da ke zargin jami’an DSS da sace Sanata Melaye daga hanun ‘yan sanda a asibiti.

Ya kuma ce, DSS tana mai bayar da tabbaci wa jama’an kasa na ci gaba da gudunar da aikinta bisa kwarewa da sanin hakkin dan adam ba tare da tauye ma wani hakkinsa na rayuwa ko walwala ba.
Source: hausa.leadership.ng

Saturday, 12 January 2019

Duba Matakan Da Zaka Bi Domin Yin Rejistar 2019 UTME - JAMB

Hukumar da ke kula da zana jarabawar share fagen shiga manyan makarantu na gaba da sakandire (JAMB) ta fara sayar da takardar cike gurbin karatu a manyan makarantu, a zango na 2019 (UTME).

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa, da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter @JAMBHQ. Ga hanyoyi 6 da dalibai zasu bi don yin rijistar jarabawar.

1. Babu wani dalibi da aka yarje mashi ya yaje wata cibiyar zana jarabawar (CBT) ba tare da ya fara kirkirar shafinsa na kansa a shafin yanar gizo na hukumar ba.

2. An shawarci dalibai su kirkiri shafikansu ta hanyar aika sakon karta kwana, mai dauke da suna (sunan farko, suna na biyu da suna na tsakiya) zuwa ga lamba: 55019

3. Bayan an aika wannan sako, a dan jira na wani lokaci, za a samu sako ya shigo, mai dauke da lambobi 10 a jiki, lambobin ne mabudin shafin dalibi.

4. Za a yi amfani da wadannan lambobi (code) guda 10 da aka turo wajen sayen takardar neman gurbin karatun a wuraren da akaje sayen takardar, walau bankuna, MMOs, MFBs, da dai sauransu.

5. Bayan sayen wannan takarda, za a aikawa dalibi sako a wayarsa, mai dauke da wasu lambobin sirri na bude takardar gurbin karatun (e-pin).

6. Dalibi zai gabatar da wadannan lambobin sirri (e-pin) a cibiyar da aka amince a zana jarabawar JAMB mafi kusa da kai, don yin rejista kai tsaye. Haka zalika JAMB ta samar da sunaye da adireshin dukkanin cibiyoyin zana jarabawar data amince da su a fadin kasar. Dalibai su duba shafin hukumar na yanar gizo don ganin cikakken sunayen cibiyoyin da ke mafi kusa da su.

Wata Kungiya Ta Nemi Buhari Ya Kara Ma Sufeto Janar Na ‘Yan Sandan Wa’adi

Ambasada Mukhtar Gashash, wanda yake shi ne shugaban kungiyarnan ta ‘Eminent Persons’ Forum’ reshen jihar Kano sun yi kira da babbar murya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara wa’adin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya, wato Ibrahim Idris.

Sun yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da suka kira wanda ya jagoranci kungiyoyin da ba na gwamnati ba, kungiyoyin kare hakkin al’umma, da sauran su a jihar Kano a Jiya Alhamis.

Mukhtar Gashash ya ce; wannan kira ya zama wajibi ne saboda irin nasarorin da shugaban ‘yan Sandan ke kawo wa kasarnan a bangaren tsaro ta hanyar kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasarnan.

Suka ce; da wannan suke kira ga shugaban kasar da kuma ‘yan majalisar kasar da a kara wa’adin Sufeto Janar na ‘yan Sandan.

Friday, 11 January 2019

MUSIC: Sagy Ft. Dj Ab – Show You Love

The talented and fastest rising singer known as SAGY collaborates with the prolific Northern Nigerian rapper DJ AB blessing our speakers with a unique and melodious song titled “SHOW YOU LOVE”. Enjoy!

Wednesday, 9 January 2019

Jama’a Ba Za Su Yi Nadamar Sake Zaben Jam’iyyar APC Ba - Gwamna Masari

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa idan ‘yan Najeriya suka sake zaben jam’iyyar APC a wannan zaben mai zuwa ba za su yi nadamar yin hakan ba.

Gwamna Masari yana magana a gaban dandazun magoya bayan jam’iyyar APC a wajan gangamin yakin neman zabensa karo na biyu da ya gudana a kananan hukumomin Matazu da Musawa domin tunkarar zabe mai zuwa.

Kamar yadda ya bayyana a karkashin jagorancin gwamnatin APC an kawo canji mai ma’ana wanda ya canza rayuwar ‘yan Najeriya ta yau da kullin inda ya kara da cewa mafiyawancin alkawarin da suka dauka a shekarar 2015 sun cika saura kuma suna kan hanya cikawa Sannan ya bada tabbacin cika alkawari da jama’ar suka roka a wannan yakin neman zabe na shi, da zaran an samu nasasar lashe zabe a wannan zabe mai zuwa.

Haka kuma gwamna Masari ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da ya samu a cikin shekaru uku da rabi da ya hau karagar mulki musamman a bangarorin da ya ba mahimmanci A kananan hukumomi gudan biyun da aka kai ziyarar yakin zaben an karbi dubban ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da suka canza sheka zuwa jam’iyyar APC wanda shugaban jam’iyyar na jihar Shitu S. Shitu ya ce yanzu sun zama ‘ya ‘yan jam’iyyar APC babu banbanci da wadanda aka haifi jam’iyyar tare da su.

Sannan ya yi kira ga jama’a da su tabbatar sun zabi jam’iyyar APC a zabe mai zuwa domin ganin anci gaba da samun nasasar da aka sa gaba sabodda amfanin al’umma da kasa baki daya Kazalika gwamna Aminu Bello Masari ya buda hanyar da ta tashi daga mararrabar Sayaya zuwa garin mazoji mai tsawon kilomita 24 wanda daman tana cikin alkawuran da Masari ya dauka.

Source: hausa.leadership.ng

Za A Fara Bukatar Katin Dan Kasa Wajen Gudanar Da Harkokin Gwamnati

Hukumar bayar da lambar sheda ta kasa ta NIMC ta sanar da cewar, yin amfani da lambar sheda ta kasa ta NIN a tsakanin hukumimin gwamnati za ta fara aiki daga ranar daya ga watan Janairun shekarar 2018.

Darakta Janar na hukumar ta NIMC, Aliyu Aziz ne ya sanar da hakan, inda ya ce, hakan ya nuna cewar, ma’aikatun gwamnati, hukumimi da kuma sassa sun dauki bayanan sun kuma gabatar da lambar ta sheda saiko wanne dan kasa ya bukaci lambar kafin a gudanar masa da duk wani aiki da yake bukata.

Aliyu Aziz ya kuma baiwa yan Nijeriya tabbacin cewar, babu wani dan kasa da za’a haramta masa samu wani gudanar da aikin gwamnatin don bai mallaki lambar shedar ba.

Ya ci gaba da cewa, karbar lambar shedar ko tattara bayanan irin wadannan hukumomin gwamnati ko ajent dinsu da kuma fannin masana’antu masu zaman kansu da aka sanya su a cikin tsarin na hukumar, zai taimaka wajen tattara bayanan su.

Acewar sa, ma’aiakatun dakuma hukumomin, sun hadada, fannonin ilimi, Sufurin sama, ofishin shugabar ma’aiakata ta na kasa, ofishin Akuwa na tarayya, hukumar kididdigar alumma ta kasa, hukumar zabe, hukumar yin rijistar sana’oi ta kasa, hukumar tara haraji ta kasa da kuma hukumar sadarwa ta kasa.

Sauran ya ce, sun hadada, shirin lafiya na kasa, hukumar EFCC, hukumar shirya jarrabawa ta kasa JAMB, rundunar yansanda ta kasa da kuma hukumar musayar kudi ta kasa SEC.

Aliyu Aziz ya kara da cewa, hukumomin da aka zayyana a sama, dole ne su bukaci su kuma tantance lambar shedar ta NIN wadda tuni aka amice da ita a tsarin hada-hadar bankun na kasar nan, hukumar kula shege da fece ta kasa, hukumar kiyaye hadurra ta kasa da kuma hukumar fansho ta kasa.

Ya sanar da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma majalisar zantarwa ta kasa tuni suka amince da sabon tsarin na NDIESR don sanya yan Nijeriya da kuma mazauna don a sanya su a cikin bayanan na shedar.

Aliyu Aziz ya kara da cewa, “an dora mana nauyin yiwa daukacin yan Nijeriya rijista da kuma wadanda suka zaune a cikin kasar a bisa izinin hukuma ko kuma a kalla sama da kashi 95 bisa dari na alummar kasar nan a cikin shekaru uku masu zuwa.

Ya bayyana cewar, ba wai lallai bane sai hukumar ta kakkafa cibiyoyi da ofishoshi a daukacin fadin kasar nan ba, musamman idan aka yi la’akari da halin tattalin aezikin kasa da ake fuskanta a yanzu.

A bisa tausayi na gwamnatin tarayya, ta amince da sabon tsarin na NDIESR wanda zai tabbar da kuma dorawa dukkan ma’aikatun gwamnati da hukumomin da aka zayyana a sama da kuma masana’antu masu zaman kansu na hukumar ta yi masu lasisi da hukumar don tattara bayanan yan kasa ta hanyar basu lambar shedar ta kasa.
Source: hausa.leadership.ng

Tuesday, 8 January 2019

Ba Da Ni A Ka Yi Wa Buhari Ihu A Majalisa Ba – Dino Melaye

Sanatan nan da ake ta faman kwaramniya da shi, mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye, ya musanta rahotannin da kafafen yada labarai na yanar gizo suke yadawa da ke cewa yana daga cikin ‘yan Majalisun tarayyan da suka yi wa Shugaba Buhari, ihu a ranar 19 ga watan Disamba.

Wasu daga cikin ‘yan Majalisun na tarayya sun yi wa Buharin ihu a lokacin da yake gabatar wa da Majalisun kasafin kudin 2019, a wannan ranar, inda suka nemi su rika yin wasu kalaman batunci a gare shi.

Amma Melaye, wanda a halin yanzun yake farfadowa a wani Asibitin ‘yan sanda da ke Abuja, ya ce, ba zai yiwu a ce yana cikin wadanda suka aikata hakan ba, saboda shi ai ba ma shi a wajen zaman.

Cikin sanarwar da Sanatan ya fitar ta hannun mai taimaka masa ta fuskacin manema labarai, Gedion Ayodele, cewa ya yi, ba yana karyata hakan ne domin tsoron wani abu ba, sai dai don ya gyara gaskiyar maganar ce kadai.

A baya, Melaye ya ki ya karyata batun ne domin ya san tsegumi ne kawai irin na yanar gizo ba komai ba, amma ai Sanata Melaye, ba ma shi a cikin Majalisar sam a wannan ranar.

A kan radin kansa ne Sanata Melaye, ya gabatar da kansa ga ‘yan sanda a ranar Juma’a, bayan kwanaki takwas ‘yan sandan suna yi wa gidansa kawanya a Abuja.

A nan take kuma sai ya fadi kasa a some, inda aka yi gaggawan garzayawa da shi Asibitin na ‘yan sanda domin neman magani. Rundunar ‘yan sanda ta aike da jami’anta 60 a Asibitin da ke Garcia, Abuja, inda ake duba lafiyar ta Melaye.

Bayan da Likitocin Asibitin ne suka tsayu a kan Melaye, sai ya sami farfadowa, a bayan suman da ya yi jim kadan a fara masa tambayoyi a ofishin na ‘yan sanda da ke Guzape, Abuja.

Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa, jami’an kula da lafiyar na shi suna tunanin sai an yi masa gwajin, ‘cardiopulmonary,’ a sakamakon wasu abubuwan da Likitocin asibitin suka yi la’akari da shi.

Ana jin cewa, kila Liktan Asibitin ya bayar da shawarar a mayar da shi wani Asibitin kwararru inda suke da mahimman kayan aikin da za su iya kulawa da Melayen sosai.

Yan sandan sun ce ne, suna neman Melaye a bisa zargin da suke yi ma shi na harbin wani dan sanda mai suna, Sajan Danjuma Saliu, wanda ke aiki a sashen ‘yan sandan kwantar da tarzoma, bataliya ta 37, a sa’ilin da yake kan aikin tsayarwa da bincikar ababen hawa a kan titin, Aiyetoro Gbede, Mopa, Jihar Kogi.

Source: hausa.leadership.ng

Monday, 7 January 2019

Yan Bindigar Zamfara Na Da Alaka Da Boko Haram - Ministan Tsaro

Ministan Tsaro, Birgediya Janar Mansur Dan-Ali (mai ritaya), ya ce, ba za a iya yanke hukunci kan cewa babu alaka a tsakanin kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma ‘yan ta’addan da suke ta aiwatar da nau’ukan ta’addanci a Jihar Zamfara ba.

Da yake magana da manema labarai a ziyarar gani da ido da ya kai a Jihar ta Zamfara, Ministan cewa ya yi, a kowane lokaci, ‘yan ta’adda sukan nemi taimako ta wasu hanyoyin, ya kara da cewa, mahimmin abu dai shi ne mu samar da hanyar tsare kan iyakokin kasar nan.

Ya ce, ya zo ne domin ya gana da rundunonin da ke wajen domin sanin ainihin irin kalubalen da suke fuskanta da sauran matsalolin su domin sanin hanyar da ya kamata a bi. “Dawowa na kenan daga kasar Cadi, mun tattauna da su.

Mu na kan tattaunawa da kasashen da ke makwabtaka da mu, Nijar da Kamaru, domin tabbatar da tsaron kan iyakokinmu ta fuskacin kai da komowan makamai, wanda na tabbata yana da matukar mahimmanci a kan kalubalen ‘yan ta’adda a Nijeriya,” in ji shi.

A cewar sa, ko da za a kawo Sojoji milyan guda ne a Jihar, ba zai amfanar ba, har sai masu ruwa da tsaki na Jihar sun shirya hanyar neman zaman lafiya.

Ministan ya ce, kamata ya yi a ce an kafa rundunonin fararen hula ‘yan sa kai tun da jimawa, ba wai sai a yanzun ba, domin ai Sojoji ba su lakanci yanda wuraren suke ba sosai, hakan ne ya sanya ake kashe su, ba a horas da su a kan su yi kisa ba, su ma ai Mutane ne. An horas da Soja ne domin ya kawo zaman lafiya.”

Source: hausa.leadership.ng

Sojoji Sun Yi Wa Ofishin DailyTrust Dirar Mikiya A Abuja Da Borno

Jiya da yamma ne kwambar sojoji suka yiwa hedikwatar Media Trust, mawallafan jaridar DailyTrust da ke babban birnin tarayya, Abuja dirar mikiya.

Haka kuma makamancin wannan farmaki na sojojin Nijeriyan ya rutsa da ofishin yanki na kamfanin jaridar Daily Trust da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno, yayin da suka yi awon gaba da editan yanki- Uthman Abubakar da wakilin jaridar da ke jihar, Ibrahim Sawab.

Duk da ba a san dalilin da ya jawo daukar wannan mataki ba, amma ana alakanta matakin da wani rahoton da jaridar ta buga na ranar lahadi- dangane da yakin da sojojin ke yi a arewa maso-gabacin Nijeriya.

Kamfanin Daily Trust shi ne ya fitar da sanarwar samamen da yan sojan suka kai a ofishin ta- jim kadan da faruwar lamarin tare da karin bayani da cewa, sojojin sun wancakalar da kofar shiga ofishin ta na yanki ka ke Maiduguri, da karfin dawo-dawo, kana sun yi awon gaba da editocin ta guda biyu.

Wani ganau a wajen ya tabbatar da yadda ya ganewa idon sa zuwan sojoji a ofishin tare da yadda suka bukaci a hannunta musu editan lamurran siyasa a ofishin- Hamza Idris, wanda suka zarga da rubuta wancan labarin.
Source: hausa.leadership.ng

Gaskiyar Dangantakar Buhari Da Amina Zakari

A jiya Juma’a ce gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa, babu wata dangantaka ta jin tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Amina Zakari wadda aka nada ta zama shugaban cibiyar tattara zaben shugaban kasa wanda za a yi a watan Fabariru mai zuwa.

“Shugaban kasa Buhari ba shi da dangantaka ta jini tsakaninsa da kwamishinar cibiyar tattara zaben shugaban kasa Amina Zakari,” Babban Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman a kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka jiya Juma’a a Abuja.

“An dai samu auratayya ta nesa a cikin zuri’arsu amma cewa shugaban kasa na da dangantaka ta jini tsakaninsa da kwamishinar karya ce kawai,” inji shi.

In za iya tunawa dai an nada Amina Zakari ranar Alhamis din da ta gabata ta shugabanci Cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa a hukumar zabe mai zaman kanta wanda za a yi a watan Fabarairu mai zuwa.

Wannan matsayi da aka ba Amina ya tayar da kura a siyasar nijeriya, inda jam’iyyar adawa ta PDP ta nuna cewa, ita Amina ‘yar uwar Buhari ce, saboda haka suke zargin ya daukota ne ta yi masa aiki.

Sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP ya soki lamirin nadin Aminar inda y ace wannan kamar yi wa dimokaradiyya zagon kasa ne.

Shi kuma da yake mayar da martini kan wannan bayani, Malam, Shehu ya ce, wannan Magana da jam’iyyar ta PDP ke yi, Magana ce wadda bat a da tushe balle makama.

Source: hausa.leadership.ng

ASUU Ta Amince Malaman Jami’a Su Yi Wa INEC Aiki

Kungiyar malaman jami’a, ASUU, ta tabbatar wa da hukumar zaben Najeriya, INEC, amincewarta kan malaman jami’a, wadanda mambobinta ne, cewa za su iya yi wa INEC din aikin zabe koda kuwa kungiyar ba ta daina gudanar da yajin aikin da ta ke yi a halin yanzu ba.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin hukumar zaben a karshen makon nan a wata sanarwa da ta bayar bayan kammala ganawa da shugabannin ASUU na kasa a hedikwatar kungiyar da ke Abuja.

Da alama wannan sanarwar babban albishir ce ga kasar, domin hakan zai rage fargabar da a ke da ita ta yiwuwar kawo cikas ga tafiyar da shirye-shiryen babban zabe na shekara ta 2019 da ke tafe a watan Fabrairu.

Idan dai za a iya tunawa, INEC ta saba yin amfani da malaman jamiar ne a lokacin manyan zabuka irin wadannan, inda ta ke nada su a matsayin manyan jami’an zaben nata a jihohin kasar, don tattaro ma ta sakamakon zaben da a ka kada.

“ASUU ta amince ta kyale mambobinta su yi aikin babban zaben 2019 a matsayin ma’aikata na wucingadi, duk da yajin aiki na kasa bakidaya da a ke yi a kasar,” in ji sanarwar INEC din.

Ta wara da cewa, “hakan ya biyo bayan rokon da shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci tawagar manyan kwamishihonin hukumar, kwararrun jami’ai da daraktoci na INEC, ya yiwa shugabancin kungiyar a hedikwatar ASUU da ke Jami’ar Abuja ranar Juma’ar 4 ga Janairu, 2019.”

Farfesa Mahmood ya nuna farin cikinsa kan wannan cigaba da a ka samu a lokacin da ya kai ziyarar, wacce tamkar ganin gidana, idan a ka yi la’akari da cewa shi ma malamin jami’a ne kuma wanda ya bayar da tasa gudunmawar ga cigaban ilimi a lokacin da ya ke rike da mukamin babban sakataren hukumar kula da gidauniyar manyan makarantu ta kasa (TETFUND).

A lokacin da ya ke rokon shugabannin ASUU din, Mahmood ya tunatar da su cewa daga ranar 4 ga Janairu zuwa lokacoin zabe kwanaki 42 ne kacal, kuma za a gudanar da zaben nan a mazabu 1,558 da akwatinan zabe har 119,973 da ke cibiyoyin zabe har guda 9,809 a fadin kasar cikin kananan hukumomi 774 da ke jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin kasar Abuja.

Don haka sai ya nanata mu su cewa, wannan ba karamin aiki ba ne, wanda ya ke bukatar sadaukarwa daga kungiyar da kuma malaman su kansu.

A yayin da ya ke mayar da jawabi, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, sai ya tabbatar wa da hukumar cewa kungiyar ba za ta hana mambobinta shiga aikin babban zaben kasar ba.

Ya ce, “ASUU ba za ta taba yin wani abu wanda zai kawo cikas ga shirin babban zaben kasa ba, domin kungiyar a kullum ta na bayar da gudunmawarta ne ga wanzuwar dimukradiyya a Najeriya.

“Yajin aikinmu bai hada da INEC da babban zaben kasa ba. Zai zama daya daga cikin manyan laifuka ga sashen ilimi, musamman jami’o’in gwamnati mu shiga adawa da hakan. Haka zalika, yajin aikinmu ba zai shafi harkokin bincike da kyautata wa al’umma ba.

Ya kara da cewa, “dangantakarmu da INEC ta na nan tun gabanin mulkin shugabancin INEC na yanzu. Tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya na shawartar ASUU kuma mun taimaka ma sa tun a zaben 2011.”

An dade a na fargabar ko yajin aikin da malaman jami’a su ke yi a Najeriya zai kawo cikas ko sauyi ga babban zaben kasar, amma a yanzu da alamu dai hakan ya kau.
Source: hausa.leadership.ng

Gobe Gwamnatin Tarayya Za Ta Cigaba Da Tattaunawa Da ASUU

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce, zaman tattaunawa a tsakaninta da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) zai ci gaba da gudanuwa a gobe Litinin domin ci gaba da neman shawo kan yajin aikin da kungiyar ke ci gaba da yi domin ganin an shawo kan matsalar.

Ministan ayyuka, Sanata Chris Ngege shine ya shaida hakan a cikin sanarwarsa da ya rabar wa ‘yan jarida a jiya Asabar, wanda Daraktan yada labaran ma’aikatar Mista Samuel Olowookere, ya rattaba wa hanu.

Kamar yadda sanarwar ke cewa, zaman gawar za a yi ta ne domin shawo kan yajin aikin da kuma tattauna yadda za a yi kungiyar ta koma bakin aikinta.

Sanarwar take cewa; “Ministan aiyuka Sen. Chris Ngige ya tsara ganawa da shugabanin kungiyar ASUU domin tattauna yadda za a samu bakin zaren shawo kan yajin aikin da suke yi.

Za a yi ganawar ne a ranar 7 ga watan Janairun 2019 a dakin taro na ma’aikatar aiyuka da misalin karfe 20:30 na dare daidai,” Inji sanarwar.

Kamfanin dallancin labarai ta kasa NAN ta habarto cewar ASUU dai ta shiga yajin aikin sai baba ta gani ne tun a ranar 5 ga watan Nuwamban 2018 biyo bayan gaza cika musu alkawuran da suka yi da gwamnati tun a shekarar 2009.

Source: hausa.leadership.ng

Sunday, 6 January 2019

Barcelona Ta Amince Da Daukar Rabiot Daga PSG

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta cimma yarjejeniya da dan wasan kasar Faransa, Adrien Rabiot domin yakoma kungiyar a karshen kakar wasannan da ake bugawa.

Dan wasan dan kasar Faransa wanda baije gasar cin kofin duniya ba yanada damar tattaunawa da kungiyoyin da suke son daukarsa bayan da ya rage saura watanni shida kwantaraginsa ya kare da kungiyar ta PSG.

Kungiyoyin firimiya da suka hada da Liverpool da Tottenham da kuma kungiyar Arsenal dai sune suke zawarcin dan wasan sai dai daman tuni aka bayyana cewa yafison komawa Barcelona da buga wasa.

A satin daya gabata ne dai rahotanni suka bayyana cewa dan wasan ya kammala cimma yarjejeniya da dan wasan amma daga baya kungiyar ta karyata labarin inda ta bayyana cewa babu wata Magana tsakaninta da dan wasan.

Kawo yanzu dai tuni aka bayyana cewa Barcelona ta kammala Magana da dan wasan kuma zai koma bugawa kungiyar wasa idan an kammala kakar wasan da ake bugawa inda kuma zai karbi albashi mai yawa wanda ba’a bayyana ba.

Kungiyar PSG dai tayi kokarin sake sabuwar yarjejeniya da dan wasan sai dai rashin tabbacin buga wasanni akai-akai yasa dan wasan ya nuna bazai zauna ba kuma yana bukatar sabuwar kungiya.

Source: hausa.leadership.ng

Aisha Buhari Ta Kaddamar Da Yakin Neman Zaben 2019 A Kano

Ranar Asabar din nan Mai dakin Shugaban Kasa Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta jagoranci kaddamar da yakin menan zaben shekara ta 2019 wanda kwamitin tsare tsaren yakin neman zabe bangaren mata ya gudana a Kano.
Da ta ke gabatar da Jawabinta awuri taron Hajiya Aisha Buhari ta jadadda farin cikin bisa yadda al’ummar kasar nan ke baiwa gwamnatin Buhari goyon baya.
Tace ta shirya shiga cikin kwamitin yakin neman sake zabar mai gidan na ta ne sakamakon hangen da ta yi na abubuwan alhairi da wannan gwmanati ke samawa matasan kasar nan.
Hajiya Aisha Buhari tace zuwa yanzu Gwamnatin Muhammadu Buhari ta bujiro da ayyuka iri daban daban domin koyawa mata da matasa sana’u iri daban daban, tare raba masu tallafi, haka kuma akwai wani tsari wanda ke gudana karkashin ofishin mataimakin Shigaban kasa Yemi Osinbajo wadda ake rabawa matasa Naira dunu talatin talatin domin fara dogoro da kansu, tace tana da yakinin wannan shiri idan aka Sake zabar Muhammadu Buhari za’a ci gaba da aiwatar da wannan kyakkyawan shiri.
Shi ma Gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatarwa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyar Jihar Kano na bashi kuri’a miliyon biyar a zabe shekara ta 2019, yace jama’ar Kano mutane masu godiya kuma nan ne cibiyar Jam’iyyr APC saboda haka muna da yakinin idan Allah ya kaimu lokacin zabe mai zuwa jihar Kao ce zata fara kawo sakamakon zaben wanda muke da yakinin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai lashe zaben.
Ita ma mai dakin Gwamnan Kano Dakta Hjaiya Hafsat Umar Ganduje ta bayyana sake zabar Muhammadu Buhari da Gwamna Ganduje a matasayin farar dabara, tace yanzu haka Jihar Kance Jiha daya Tilo data samarwa da mata masu tarin yawa sana’u da kuma jari a fannonin sana’a iri daban-daban, don haka sai ta godewa mai dakin shugaban kasar bisa zabar jihar Kano a matsayin wurin da za a kaddamar da yakin neman zaben shugaban Kasa a shekara ta 2019.
Cikin wadanda su ka dafawa matar shugaban kasar akwai matan gwamnonin jihohin Kano, Katsina, Kebbi, Kaduna, Jigawa da kuma mai dakin gwamna jihar Imo Rochas Okorocha a lokacin kaddamar da yakin neman zaben na shiyyar AREWA maso Yamma da a ka gudanar a babban dakin taro na Sani Abacha.

Source: hausa.leadership.ng