Friday, 25 January 2019

Monaco Ta Sallami Kocinta Thierry Henry

Tags

Kungiyar Monaco ta sallami kocinta Thierry Henry, bayan wasa 20 da ya ja ragamarta.

A ranar Alhamis Monaco ta sanar da cewar ta dakatar da kocin, amma BBC ta fahimci cewar hanyoyin rabuwa da Henry kungiyar ke bi cikin ruwan sanyi, tuni aka ce ya kama gabansa.

Ana sa ran Leonardo Jardim zai karbi aikin jan ragagamar Monaco, wanda wata uku baya aka kore shi, Henry ya gaje shi.

Monaco ta bai wa Franck Passi aikin rikon kwarya, wanda ta dauka aikin mataimakin Henry a ranar 20 ga watan Disamba, kuma shi ne zai horas da 'yan wasa a ranar Juma'a.

Source: www.bbc.com/hausa


EmoticonEmoticon