Sunday, 3 February 2019

Yadda Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Yi Hatsarin Jirgin Sama

Tags

Jirgi mai saukar ungulu dauke da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi hatsari a jiya Asabar, inda ya fado daga sama a daidai garin Kabba da ke jihar Kogi.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, ne ya tabbatar da afkuwar wannan hatsarin na fadowar jirgin ta kafar sadarwa na Twitter.

Laolu Akande ya kara da cewa, sai dai Allah ya kiyaye, domin kuwa da mataimakin shugaban kasa da sauran ’yan tawagar nasa sun tsallake rijiya da baya, domin sun fito ba tare da raunuka ba.

Ya kara da cewa, “jirgin helikwaftan Mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo ya fado a daidai Kabba, amma da shi da dukkanin ’yan tawagarsa su na cikin koshin lafiya,” kamar yadda Akande ya wallafa a shafin Twitter.

Ya kara da cewa, duk da hakan, Farfesa Yemi ya cigaba da gudanar da harkokin da su ka kai shi jihar ta Kogi.

“Ya cigaba da gudanar da ayyukan da a ka tsara wadanda su ka kai shi Kogi a wannan rana,” in ji shi.

Wakilinmu ya gano cewar, mataimakin shugaban kasar dai ya kama hanyarsa ta zuwa taron ganawa da masu ruwa da tsaki a garuruwan Kabba, Okene da Idah domin cigaba da gangamin yakin neman sake zabansu a karo na biyu ne.

Jirgin Helikwaftar dai ya fado kasa ne a lokacin da matukin ke kokarin ya sauka a filin wasa na Kabba Stadium.


EmoticonEmoticon